Iran ta bakin Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Kan sha’anin Shari’a da Harkokin ketare, Kazem Gharibabadi, ya mayar da martani kan kalaman Amurka na baya bayan nan da ya kira Kotun Hukunta Laifuka Ta Duniya (ICC) da”mai cin hanci da rashawa.”
Mista Gharibabadi , ya ce: “Sun kira Kotun da dandalin ‘ cin hanci da rashawa’ ne saboda ta na neman gurfanar da fira ministan Isra’ila B Netanyahu.”
Wannan na zuwa ne bayan da membobin Kotun suka kaɗa kuri’ar cire mai gabatar da kara na kotun, Karim Khan, a daidai lokacin da Amurka da masu fafutukar kare hakkin Yahudawa suka yi ta matsa masa lamba.
Wannan kuri’ar ta zo ne a karshen dogon bincike kan zarge-zargen cin zarafin mata wanda Wata mata ce da ke aiki da Khan a Kotun ta shigar.
Karim Khan ya sha musanta wadannan zarge-zargen kuma Lauyoyinsa sun yi Allah wadai da abin da suke ganin rashin adalci.
Dan asalin Birtaniya kuma fitaccen lauya an zabe shi a shekarar 2021 a wa’adin shekaru tara a matsayin shugaban Ofishin Mai Gabatar da Kara na Kotun, wanda ke da alhakin bincike da gurfanar da mutanen da ake zargi da laifukan kasa da kasa.
Karim Khan shi ne mai gabatar da kara wanda ya nemi sammacin kama Fira Ministan gwamnatin Sahayoniya Benjamin Netanyahu, da tsohon ministan yakinsa Yoav Gallant, bisa zargin laifukan yaƙi a Gaza, da wasu kungiyoyin kasa da kasa suka danganta da kisan kare dangi.
Reuters ta ruwaito shekaru biyu da suka gabata cewa fitowar wadannan zarge-zargen akan Khan sun zo daidai da bukatar sammacin kama Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro na lokacin a majalisar ministocinsa.
Kamfanin yada labarai na Middle East Eye ya kuma wallafa wani kamfen na tsoratarwa da aka yi wa wannan mai gabatar da kara na Burtaniya saboda bincikensa kan laifukan yakin Isra’ila a Gaza.