Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan tehran ta kira mataimakin jakadan kasar Ukraine a birnin Tehran don gabatar da korafi kan harin da sojojin kasarsa suka kai kan jirgin kasuwanci na kasar Iran a tekunb Caspian a ranar Asabar da ta gabata, wanda ya kai ga rasa ran mutum guda da raunata wasu.
Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar iran ya kara da cewa darakta mai kula da sashen kasashen gabacin Turai a ma’aikatar ne ya aikawa mataimakin jakan kasar ta Ukraine, inda bayan halattarsa ya gabatar da korafin, ya kuma fada masa abinda sojojin kasar Ukraine suka yi ya sabwa dokokin MDD kuma gwamnatin kasar Iran ba za ta taba barinsa ya wuce ba tare da ta dauki fansa ba.
JMI ta bayyana fushinta ga kasar Ukraine wacce ta dade tana talakalar kasar, dangane da yaki da kasar Rasha ta kuma zarginta da taimakawa kasar ta Rasha a kanta, wanda duk ba gaskiya bane.
Don haka JMI ta yi allawadai da harin ta kuma kara da cewa bayan ta sabwa sashe 2(4) na dokokin MDD kan diyaucin kasashe, abinda Ukraine ta yi keta hurumin JMI.