Yan Majalisar Dokokin Kasar Burtania Ta Bukaci A Dorawa HKI Takunkuman Tattalin Arziki

Yan majalisar dokokin kasar Burtania fiye da 80 ne suka bukaci gwamnatin kasar ta dorawa HKI takunkuman tattalin arziki saboda dawo da zaman lafiya a

Yan majalisar dokokin kasar Burtania fiye da 80 ne suka bukaci gwamnatin kasar ta dorawa HKI takunkuman tattalin arziki saboda dawo da zaman lafiya a duniya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto tashar talabijan ta ‘Rusiyal yau’ ya cewam Rechard Bergun wani dan majalisar dokokin kasar ta Burtania ya shaida mata cewa fiye da yan majalisar dokokin kasar 80 ne, daga majalisar wakilai da kuma wadanda ake kira loards suka sanya hannu a kan takardar bukatar gwamnatin kasar ta dorawa HKI takunkuman sayar mata da makamai, hanata ayyukan ta’addancin da take aikatawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma yanda take kissan Falasdinwa a yankunansu da ta mamaye.

Yan majalisar sun dauki wannan matakin ne bayan tattaunawa na yan kwanaki a tsakaninsu, dangane da abinda suka kita ‘takunkumi don samar da zaman lafiya’. Wanda jam’iyyar Labour ko ma;aikata gabatar, inda ta bukaci a ladabtar da yahudawa yan share wuri zauna a kasar Falasdinu da aka mamaye.

A halin yanzu dai kasashen duniya da dama suna takurawa HKI don ta kawo karshen kiyan kiyashin da take aikatawa kan al-ummar Falasdinu ,musamman a cikin shekaru 3 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted