Tehran Ta Mayar Wa Amurka Martani Kan Kotun ICC

Iran ta bakin Mataimakin Ministan Harkokin Wajen kasar Kan sha’anin Shari’a da Harkokin ketare, Kazem Gharibabadi, ya mayar da martani kan kalaman Amurka na baya bayan nan da ya kira Kotun Hukunta Laifuka Ta Duniya (ICC) da”mai cin hanci da rashawa.” Mista Gharibabadi , ya ce: “Sun kira Kotun da dandalin ‘ cin hanci da […]
Kasar Chadi ta fice daga kotun ICC

Chadi ta bi sahun kasashen Venezuela, Burkina Faso, Mali da Nijar wajen ficewa daga Kotun Hukunta Mayan Laifuka ta Duniya. A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta fitar a wannan Litinin ta zargi kotun ta ICC ko CPI da rashin alkibla da kaucewa sharudan da aka kafa ta, hasali ma da zama wacce […]
Siriya : Al-Sharaa ya tabbatar da tattaunawa da Isra’ila kan tsaro

Shugaban Siriya Ahmed al-Sharaa ya tabbatar da cewa Damascus tana aiki tukuru don kammala yarjejeniyar tsaro da Isra’ila, tare da halartar wasu kasashe masu shiga tsakani. A cikin wata hira da Al Jazeera, ya yi fatan wannan tattaunawar na iya zama matakin farko zuwa ga sulhun siyasa tsakanin kasashen biyu, yayin da ya tabbatar da […]
Ayyukan sojojin Isra’ila na kara tsananta a Kudancin Lebanon

wadannan ayyukan na kawo cikas ga aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma
Jagora Ya Amasa Bai’ar Dakarun Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Ina Aya. Mojtaba Khaminaei, ya bawa dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon amsa kan wasikar da suka rubuta masa, wacce a cikinta suna bayyana bai’arsu da kuma biyayya ga jagorancinsa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto matanin jawabin jagoran yana cewa, gaisuwa ga dakarun […]
Yan Majalisar Dokokin Kasar Burtania Ta Bukaci A Dorawa HKI Takunkuman Tattalin Arziki

Yan majalisar dokokin kasar Burtania fiye da 80 ne suka bukaci gwamnatin kasar ta dorawa HKI takunkuman tattalin arziki saboda dawo da zaman lafiya a duniya. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto tashar talabijan ta ‘Rusiyal yau’ ya cewam Rechard Bergun wani dan majalisar dokokin kasar ta Burtania ya shaida mata cewa […]
Sojojin Iran Sun Sami Sabbin Makamai, Garkuwan Sararin Samaniya

Kakakin sojojin JMI Burgedia Janar Mohammad Akraminia ya bada sanarwan cewa dakarunsa sun karbi sabbin makamai daga kamfanonin kera makamansu a cikin gida, wadanda zasu taimaka wajen kyautata tsaron sararin samaniyar kasar. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Akraminia yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, wadan […]
Iran Ta Kira Jakadan Ukraine A Tehran Dangane da Hari Kan Jirgin iran A Tekun Caspian

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a nan tehran ta kira mataimakin jakadan kasar Ukraine a birnin Tehran don gabatar da korafi kan harin da sojojin kasarsa suka kai kan jirgin kasuwanci na kasar Iran a tekunb Caspian a ranar Asabar da ta gabata, wanda ya kai ga rasa ran mutum guda da raunata wasu. Kamfanin […]
Shugaban Kasar Siriya Yace Yana Neman Sulhuntawa Da HKI

Shugaban kasar Siriya Ahmad Al-Shaar ya fadawa tashar talabijan ta Al-Jazeerah na kasar Qatar kan cewa, gwamnatinsa tana neman sasantawa da HKI ba tare da ta janye daga hakkin kasar na mallakar yankunan dukkan Golan ba. Kuma ba tare da shiga yaki da HKI ba. Shafin yanar gizo na Labarai Arab News ya bayyana cewa […]