Sojojin Iran Sun Sami Sabbin Makamai, Garkuwan Sararin Samaniya

Kakakin sojojin JMI Burgedia Janar Mohammad Akraminia ya bada sanarwan cewa dakarunsa sun karbi sabbin makamai daga kamfanonin kera makamansu a cikin gida, wadanda zasu

Kakakin sojojin JMI Burgedia Janar Mohammad Akraminia ya bada sanarwan cewa dakarunsa sun karbi sabbin makamai daga kamfanonin kera makamansu a cikin gida, wadanda zasu taimaka wajen kyautata tsaron sararin samaniyar kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Akraminia yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, wadan nan makaman garkuwa ce ga tsaron samaniyar kasar, Iran kari kan wadanda sojojinsuke da su. Kuma mataki ne babba a kyautata tsaron kasar daga makiya, musamman a yake yaken masu zuwa.

Janar Akraminia, ya kara da cewa bayan yakin kwanaki 40, sojojin Iran sun yi amfani da damar da suka samu kafin yaki na gaba,  inda suka kara kyautata makaman kasar da dama, daga cikin har da makaman kare sararin samaniyar kasar daga makiya.

Yace an musanya makamai da dama, inda aka sanya sabbi masu inganci a tsarin tsaron saman JMI,  ya kuma kara da cewa, a zagayen yakin da aka kammala Amurka ta gaza kaiwa ga dukkan manufofinta a mashigar ruwa ta Hurmuz, da kuma sauran mummunan manufofinta a kan kasar Iran.

Ya ce manufofin Amurka a zagayen yaki na karshe karshen nan, su hada da bude mashigar ruwa ta Hurmuz da rage karfin sojojin Iran sannan bayan haka mamaye kasar.

Yace amma sojojin Iran sun sake nuna masu cewa a shirye suke su fuskanci duk wani kokari na, kwace mashigar, ko rage karfin sosojin kasar. Banda haka, Iran ta sami nasarar korar mafi yawan sojojin kasar Amurka daga yankin yammacin Asia.

Daga karshen yace, sojojin Iran sun fidda wasu sabbin dabarbarun yaki idan makiya sun sake wani kuskuren lissafi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted