Jagora Ya Amasa Bai’ar Dakarun Kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Ina Aya. Mojtaba Khaminaei, ya bawa dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon amsa kan wasikar da suka

Jagoran juyin juya halin musulunci a nan kasar Ina Aya. Mojtaba Khaminaei, ya bawa dakarun kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon amsa kan wasikar da suka rubuta masa, wacce a cikinta suna bayyana bai’arsu da kuma biyayya ga jagorancinsa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto matanin jawabin jagoran yana cewa, gaisuwa ga dakarun kungiyar Hizbullah masu Imani da gwagwarmaya a kan tafarkin All…, ya yabawa masu kan hakuri da jurira a kan hanyar jihadi a kan tafarkin All..da suka zaba, wajen fuskantar manya manyan azzaluman duniya wadanda suka hada da Amurka da HKI.

A wata wasika da ya rubutawa shugaban kungiyar Sheikh Naem Qasim, Aya. Mujtaba Khaminaei, jihadi da kuma turjiya sune kadai zabin da ya ragewa masu son yenci da diyauci a duniya. Ya kuma yabawa marigayi shahid Sayid Hassan Nasarallah da Sayyid shahid Safiyyuddeen da kuma sauran kwamandojin kungiyar wadanda suka bada rayuwansu don hana HKI mamayar kasarsu da kuma sauran shahidai a wannan tafarkin, da kuma iyalan shaihidai da  sauran mumonai. Daga karshen ya roki All..T ya kasance tare da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted