Chadi ta bi sahun kasashen Venezuela, Burkina Faso, Mali da Nijar wajen ficewa daga Kotun Hukunta Mayan Laifuka ta Duniya.
A wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Chadi ta fitar a wannan Litinin ta zargi kotun ta ICC ko CPI da rashin alkibla da kaucewa sharudan da aka kafa ta, hasali ma da zama wacce ake juyawa yadda aka dama.
Hakan ya santa ta zama kasa ta biyar da ta fice daga Kotun a kasa da wata biyu.
Gwamnatin N’Djamena ta sanar da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya game da shawarar da ta yanke ta janye daga yarjejeniyar ta Roma da ta kafa kotun a 2002.
A cewar gwamnatin Chadi, “tun lokacin da ta fara aiki, Kotun ta bude bincike goma sha uku (13), wanda na farko ya shafi Uganda, Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, Darfur (Sudan), Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kenya, Libya, Côte d’Ivoire, Mali, da Burundi, kafin a fara shari’o’i a hankali a wasu yankuna na duniya.”
Gwamnatin Chadi ta kuma ce ta lura cewa ICC “tana da fursunoni bakwai (7) kacal, wadanda shida (6) daga cikinsu a cikin Afirka ne sai guda daya (1) kawai a wajen nahiyar.”
A cewar N’Djamena, “idan aka hada wadannan abubuwan, sun zama hujja na rashin tasirin kotun.
Sanarwar ta Chadi ta zo ne kwanaki kadan bayan da kasahen Nijar, Burkina Faso, da Mali, wadanda kewance a kungiyar Sahel (AES), suka sanar da ficewarsu daga Kotun a hukumance, sai kuma Venezuela da ita ta sanar da ficewa daga kotun.
An kafa Kotun ta (ICC), kotun, a shekara ta 2002 kuma hedikwatarta tana Netherlands, saidai a cikin ‘yan shekarun nan, tana fuskantar suka game da yanayin zaben shari’o’in da take saurara.
Kafin hakan dama Kasashe irinsu Burindi a shekarar 2017, da Philippines a shekara ta 2019, sun kammala ficewarsu daga Kotun.