Shugaban kasar Siriya Ahmad Al-Shaar ya fadawa tashar talabijan ta Al-Jazeerah na kasar Qatar kan cewa, gwamnatinsa tana neman sasantawa da HKI ba tare da ta janye daga hakkin kasar na mallakar yankunan dukkan Golan ba. Kuma ba tare da shiga yaki da HKI ba.
Shafin yanar gizo na Labarai Arab News ya bayyana cewa HKI ta kwace yankin duddan Golan daga hannun gwamnatin kasar syriya ne tun yakin kwanaki 6 tsakanin laraba da HKI, a shekara 1967, sannan ta maida yankin a matsayin bangare na HKI a shekara 1981.
A karon farko da shugaban kasar siriya ya yi jawabi a babban zauren MDD tun bayan fara yakin basasa a kasar a shekara 2014, shugaba Ahmad Sharaa, ya fadawa duniyakan cewa gwamnatinsa bata da wani shiri na yakar HKI kuma ba zata yaki kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ba, kamar yanda shugaba trump yake so.
Bayan faduwar gwamnatin shugaba Asad a shekara ta 2024 ne, yan tawaye masu samun goyon bayan kasashen yamma suka kwace kasar Siriya sannan Ahmad Shaar ko Abu mohammad julani ya dare kan kujerar shugabancin kasar.
Bayan haka yahudawan HKI sun mamaye sauran yankunan dukkan Golan suka kutse cikin kasar suka mamaye hatta dutsen Hermon wanda yake kallon birnin Demash babban birnin kasar.