Search
Close this search box.

Sojojin Rasha Sun Sami Ci Gaba A Fafatawan Da Suke Yi Da Ukraine A Yankin Donesk

Ma’aikatar harkokin tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa, sojojin kasar ne suke iko da garin Sviridonovka na yankin Donesk kusa da iyaka da kasar Ukraine.

Ma’aikatar harkokin tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa, sojojin kasar ne suke iko da garin Sviridonovka na yankin Donesk kusa da iyaka da kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto ma’aikatar tsaron kasar Rashan na cewa sojojin kasar Rasha sun sami nasarar dawo da ikon gwamnatin kasar kan yankunan da sojojin Ukraine suka kwace a cikin yan kwanakin da suka gabata.

Sannan mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha Mariya Zakharova ta kara da cewa makamai masu linzami da kuma jiragen yakin da ake sarrafasu daga nesa, wadanda sojojin kasar Ukraine suka cilla a kan yankunan fararen hula a Rasha, suna nufin lalata wuraren rayuwar fararen hula a Rasha ne.

Ta kuma kara da cewa shi ne ake kira ayyukan ta’addanci. Zakharova ta kammala da cewa maida martanin sojojin Rasha dangane da wadan nan ayukan ta’addanci ba zai dauki lokaci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments