Somalia ta soki furucin Burtaniya Kan ballewar Somaliland daga kasar

Ministan harkokin wajen Somalia Ahmed Moalim Faki Ahmed, ya soki kalaman jakadan Burtaniya a kasar, Mike Nithavrianakis, inda ya yi ishara da ballewar yankin “Somaliland.” Tare da bayyana hakan a matsayin katsalandan a cikin harkokin Somalia da hadin kanta ,  yana mai jaddada cewa “ba za a amince da haka ba.” Ministan harkokin wajen Somaliya, […]

Hamdan: Netanyahu Ba A Shirye Yake Ya Amince Da Dakatar Da Bude Wuta Ba

Daya daga cikin fitattun jagororin Falastinawa ‘yan gwagwarmaya Usama Hamdan ya bayyana cewa, Benjamin Netanyahu ba a shirye yake ya amince da duk wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ba. Jaridar Isra’ila ta Walla ta bayar da wani rahoto da ke cewa, Isra’ila ta yanke shawarar ci gaba da luguden wuta a yankin Gaza da […]

Hamas Da Jihadul Islami Sun Dauki Alhakin kai Harin Tel Aviv

Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa na Hamas da Islamic Jihad da ke Gaza sun dauki alhakin harin bam da aka kai a birnin Tel Aviv. A cikin wata sanarwa da ta fitar a yau, rundunar al-Qassam Brigades, reshen soji na Hamas, ta ce ta gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar dakarun Saraya al-Quds, reshen soji […]

MDD ta yi gargadi kan karuwar hare-haren da ake kaiwa ma’aikatan jin kai a Gaza

A ranar jin kai ta duniya, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin karuwar tashe-tashen hankula da kuma hare-haren da ake kai wa ma’aikatan jin kai a zirin Gaza, yayin da ake ci gaba da fuskantar yakin da Isra’ila take kaddamarwa kan al’ummar yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah-wadai da cin zarafin ma’aikatan jin kai, […]

Netanyahu yana hankoron fadada yaki domin guje wa faduwa

Parstoday – Tsohon Fira Ministan Isra’ila Ehud Barak ya kai hari ga gwamnatin Netanyahu mai tsatsauran ra’ayi kan rashin cimma matsaya da Hamas, ya kuma yi gargadin cewa Netanyahu na janyo Isra’ila cikin yakin yankin. Tashar Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, gibin dake tsakanin mahukuntan yahudawan sahyuniya na cimma matsaya da kungiyar Hamas domin […]

Jirgin Leken Asiri Na Kungiyar Hizbullah Ya Yi Shawagi Kan Gidan Natanyahu

Jirgin saman daukar hotunan leken asiri na kungiyar Hizbullah wanda ake sarrafashi daga nesa, ya yi shawagi kan gidan firai ministan HKI Benyamin Natanyahu da ke tsakanin birnin Tel-Aviv da kuma Haifa na bakin ruwa, ba tare da kayakin aikin soje na HKI da kawayenta da suke yankin sun gano shi ba. Kamfanin dillancin labaran […]

Sojojin Rasha Sun Sami Ci Gaba A Fafatawan Da Suke Yi Da Ukraine A Yankin Donesk

Ma’aikatar harkokin tsaron kasar Rasha ta bayyana cewa, sojojin kasar ne suke iko da garin Sviridonovka na yankin Donesk kusa da iyaka da kasar Ukraine. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto ma’aikatar tsaron kasar Rashan na cewa sojojin kasar Rasha sun sami nasarar dawo da ikon gwamnatin kasar kan yankunan da sojojin […]

Wani Jami’in Diblomasiyyar Kasar Burtaniya Ya Ajiye Aikinsa Saboda Kissan Kiyashi A Gaza

Wani babban jami’in diblomasiyya a ma’aikatar harkokin wajen kasar Burtaniya ya yi murabus daga mukaminsa don nuna rashin amincewarsa da ci gaban da aikawa HKI makamai wanda gwamnatin kasar Burtaniya take yi. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa Mark Smith jami’a mai kula da ayyukan yaki da ta’addanci a ofishin jakadancin […]

Hamas Ta Soki Sabuwar Yarjejeniyar Tsagaita Wuta A Gaza

Kungiyar Hamas ta zargi Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da gaza cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza, biyo bayan tattaunawar kwanaki biyu da aka yi a birnin Doha da aka kammala ranar Juma’a, wacce kungiyar ba ta shiga cikinta ba. Kungiyar ta mayar da martani a hukumance a cikin wata sanarwa da ta fitar a […]

Araqchi : Zan Samar Da Hanyoyin Tunkarar Takunkuman Da Aka Kakabawa Iran

A rana ta biyu na muhawara a majalisar dokokin Iran kan jerin sunayen ministocin da shugaban Kasar Massoud Pezeshkian ya gabatar, Abass Araqchi wanda aka gabatar a mukamin ministan harkokin wajen kasar a sabuwar gwamnatin, ya kare manyan abubuwan da ya sa a gaba, ciki har da hanyoyin tinkarar takunkumin da aka kakabawa kasar ta […]

Ana Tattaunawar Kawo Karshen Rikicin Sudan A Masar

A wani lokaci yau Litini ce ake fara tattauanwar neman tsagaita wuta a rikicin Sudan. Gwamnatin Sudan din ta ce za ta tura tawaga birnin Alkahira domin yin tattaunawa da jami’an Amurka da na Masar, a yunkurin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe watanni 16 ana yi a kasar. Gwamnatin mulkin sojin kasar, da […]