Rundunar Sojan Kasar Yemen ta sanar da harbo jirgin leken asirin Saudiyya wanda ya shiga sararin samaniyar kasar ta hanyar birnin Sa’adah, tana mai sake jaddada azamarta ta hana jiragen ruwan Saudiyyar wucewa ta mashigar Babal-Mandab.
Mai Magana da yawun rundunar sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ne ta sanar a yau Laraba cewa; Na’urorin tsaron sararin samaniyar Yemen sun kakkabo jirgin leken asiri na Saudiyya samfurin ” Caryal” a yankin Sa’adaha dake arewacin Kasar.
Sanarwar ta ce lamarin ya faru ne da safiyar yau Laraba, sannan kuma ta ce; Hakkin kasar Yemen ne ta kare kanta daga duk wani wuce gona da iri.
Gabanin kakkabo jirgin leken asirin na Saudiyya, janar Sari ya sanar da cewa sun kai wa jirgin ruwan dakon man fetur “NCC Ghazal” hari, bayan da ya keta takunkumin da Yemen ta kakaba wa Saudiyya.
Janar Sari ya ce an kai wa jirgin ruwan hari ne da makami mai linzami samfurin ” Ballistic” da hakan ya tilasta masa ja da baya.
Kasar Yemen ta hana jiragen ruwan Saudiyya wucewa ta mashigar “Babal-Mandab” ne saboda yadda Saudiyya ta dauki shekaru 11 tana hana jiragen sama sauka abirnin Sanaa, ko kuma isar jiragen ruwa zuwa tashar Hudaidah.
A cikin kwanaki kadan da su ka gabata, sojojin na kasar Yemen sun tilasta wa jiragen ruwan Saudiyya da dama sauya hanya ko kuma komawa inda su ka fito.