Sojojin Isra’ila Sun Kai Samame A Yankuna Daban daban A Gabar Yammacin Kogin Jodan

Rahotanni dake fitowa daga yankin falasdinu sun nuna cewa yankuna daban daban dake gabar yammacin kogin Jodan sun fuskanci hare hare daga sojojin Isra’ila inda

Rahotanni dake fitowa daga yankin falasdinu sun nuna cewa yankuna daban daban dake gabar yammacin kogin Jodan sun fuskanci hare hare daga sojojin Isra’ila inda suka kama falasdinawa da dama da ya kai ga harbin wani matashi bafalasdine da kuma wani datijjo guda daya a bait laham da Nablus.

Dan rahoton gidan talabijin din Aljzeera ya rawaito cewa sojojin Isra’ila sun fadawa sansanin yan gudun hijira na aqaba jabar dake kudancin garin Ariha da qalqiliya da kuma kauyen kubar dake gefen garin Ramallah da kuma garin kufr akaba da arewacin birnin Kudus.

Sojojin Isra’ila sun harba hayaki mai sa hawaye a gidajen falasdinawa a garin kariyut ,majiyar kungiyar bada agaji ta red cresant ta falasdinu ta sanar a yammacin jiya juma cewa sojojin isra’ila sun harbi wani matashi a sansanin yan gudun hijira na Dahaisha dake garin baita laham  lokacin da sojojin isra’ila suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen mamaye sansanin yan gudun hijiran

Ana sa bangaren shugaban gwamnatin kwarya kwaryan cin gashin kai ta falasdinu yayi tir da mummuna haren haren da sojojin isra’ila suka kai kan alummar falasdini a gabar yammacin kogin jodan , kana ya gargadi gwamnatin sahyuniya game da mataken da take dauka na mulkin mallaka  zai  tunzura alumma gabar yammacin kogin jodan,

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted