Sojojin Iran Sun Kakkabo Jiragen Amurka Drons Guda 2

Sojojin Iran reshen garkuwan sararin samaniya sun sami nasarar kakkabo jiragen yakin Amurka samfurin Drons guda 2 a yammaci da gabacin mashigar ruwa ta Hurmuz.

Sojojin Iran reshen garkuwan sararin samaniya sun sami nasarar kakkabo jiragen yakin Amurka samfurin Drons guda 2 a yammaci da gabacin mashigar ruwa ta Hurmuz.

Kamfanin dillancin labaran tasnim na kasar Iran ya nakalto wata sanarwan da sojojin suka fitar a jiya talata da yamma, wacce ta bayyana cewa, a aiki na farko sojojin wadanda suke da alhakin tabbatar da tsaron sararin samnaiyar yankin mashigar ruwan, sun gano jirgin yakin da ake kira Lucas a yammcin mashigar sannan suka kakkaboshi ba tare da wata matsala ba. Kuma sun yi amfani da tsarin garkuwan sararin samaniya na bai daya wanda sojojin suka samar a cikin gida don yin wannan aikin.

Sannan na biyu, kuma ya shafi jirgin yaki wanda ake sarrafashi daga nesa kuma mafi muhimmanci ga sojojin Amurka wato MQ-9, sun hango shi daga gabacin mashigar suka kuma yi amfani da tsarin garkuwan sararin samnaiya don kakkabo shi ma.

Sojojin kasar Iran sun sami nasarar kakkabo jiragen yakin Amurka wadanda ake sarrafasu daga nesa masu yawa daga ciki har da samfurin MQ-9 wanda suke tutiya da shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted