Sojojin Amurka Sun Ce An Ba Su Umarni Ne Da Su Rika Kai Wa Cibiyoyin Fararen Hula Na Iran Hare-hare

Tashar talbijin din " MS NOW" ta Amurka ta ambato majiyar sojojin Amurkan suna cewa sun sami umarnin ne dag ma'aikatar yakin Amurka ta "Pentagon
ma'aikatar yakin Amurka

Tashar talbijin din ” MS NOW” ta Amurka ta ambato majiyar sojojin Amurkan suna cewa sun sami umarnin ne daga ma’aikatar yakin Amurka ta “Pentagon ” akan su rika kai wa cibiyoyin fararen hula hare-hare.”

Tashar talabijin din ta ambato wani daga cikin sojojin da su ka yi yaki da Iran yana cewa; Rundunar sojan Amurka ta kai wa cibiyoyin fararen hula hare-hare da gangan, domin gadoji da dama da aka kai wa hari, ba su da alaka da yaki, kuma yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.”

Haka nan kuma sojan na Amurka ya ce, “ma’aikatar Pentagon” babu abinda ya dame ta da kashe fararen hula a tsawon lokutan kai wa Iran hare-hare.”

Wani daga cikin sojojin da tashar talabijin din ta “MS NOW” ta yi hira da shi ya bayyana cewa; Yakin da Amurka ta yi da Iran babu wata rawa da zai taka wajen amfanar duniya.”

Shi kuwa wani sojan ya fada wa tashar talabijin din cewa; Shugabannin Amurka na yanzu, ba mutane ne da za a iya hasashen abinda za su iya aikatawa ba.”

A ranar farko ta kallafaffen yakin Amurka akan Iran, a watan Febrairu, Amurka ta kai hari akan makarantar kananan yara ta “Minab” da ya yi sanadiyyar shahadar kananan yara da dama. Tashar talabijin din ta ce wancan harin, yana daga cikin dalilan da su ka sa sojoji da dama su ka sauya ra’ayinsu akan yaki da Iran.

A ranar Talatar da ta gabata ma dai sojojin na Amurka sun kai hari akan masu bikin aure a gundumar Hurmuzgan dake kudancin Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted