Rahotanni sun bayyana cewa farashin man dizel yayi tashin goron zabi a kasar Amurka sakamkon hare haren da take kai wa Iran, da kuma rufe mashigar Hurmuz da kasar iran ta yi, inda kusan kashi daya cikin biyar na man da ake amfani da shi a duniya yake wucewa
A jiya juma’a farashin man dezel a Amurka ya kai dala 5.85 a duk gallon daya a karon farko tun bayan harin da Amurka da isra’ila suka kai wa kasar iran a ranar 28 ga watan fabarerun shekara ta 2026,
Tashin farashin man dezel da aka fi amfanin da shi ga manyan motoci da kuma ayyukan noma da masana’antu ya jawo tashin farashin motcin zirga-zirga da kuma hauhawan farashin kayayyakin abinci da hakan yayi mummuan tasiri ga tattalin arzikin amurka kuma ya kara jawo tsadar rayuwa ga alummar kasar
masana sun yi gargadin cewa ci gaba da tashin farashin man dizel zai sanya a dauki dogon lokaci ana fama da tsadar rayuwa,
wannan matakin ya zama wani sabon kalubale ga yan jam’iyar republican a zaben tsakiyar lokaci da za’a yi a watan nuwamba mai zuwa, inda farin jinin shugaban Amurka Donald trump yayi kasa sosai saboda matsalar tattalin arziki da kasar take ciki sakamakon yakin da ya kaddamar kan kasar iran