A jiya Juma’a ne dai babban zauren na MDD ya kaddamar da sabuwar taswirar duniya wacce take nuna hakikanin girman nahiyar Afikra.
Amincewa da wannan sabuwar taswirar da babban zauren na MDD ya yi, ya biyo bayan fafutuka mai tsawo da kasashen Afirka da kuma wasu masu rajin kare manufofin nahiyar ta Afirka.
Kudurin da aka amince da shi a jiya Juma’a wanda kasar Togo ta gabatar da shi, kuma mambobin kungiyar tarayyar Afirka ( AU) su ka goya ma ta baya, ya samin amincewa kasashen babban zauren na MDD su 164.
Amurka ce ta kada kuri’ar kin amincewa da shi, sai kuma wasu kasashe shida da su zama ‘yan baruwansu. Wadannan kasashen kuwa su ne; Serbia, Estonia, Georgea, Ithuania, Moldova da kuma Ukkreniya.
A karkashin amincewa da sabuwar taswirar an yi kira ga gwamnatocin kasashe da cibiyoyi da kasa na kasa da sum aye gurbin tsohuwar taswirar da sabuwa.
Tun a cikin karni na 16 ne ake amfani da wannan taswirar ta Afirka wacce take nuna nahiyar Afirka da yankin Greenland a matsayin masu girma daya. Amma a sabuwar taswirar nahiyar Afirka ta fi yankin na Greenland girma har sau 14.
Wanda ya zana taswirar da ake amfani da ita har yanzu shi ne Gerardus Mercator domin ta taimakwa turawa su gane hanyoyin sufuri na ruwa. Sai dai an zarge shi da yin ganganci wajen fadada girman yankin dungun duniya, da Arewacn Amurka da Greenland sannan kuma ya tsuke girman Afirka da Kudancin Amurka.