Kungiyar Hamas Ta sha Alwashin Ci Gaba Da Riko Da Makamanta

isra'ila ta yi watsi da aiki da majalisar zaman lafiya da ta shiga tsakani wajen tsagaita wuta a yankin gaza
Shin kun san cewa Netanyahu ya yanke shawarar yin wasa da hankalin Yammacin duniya don ya ci gaba da mulki? Ta yaya? Ta hanyar saka musu kiyayya da Musulunci! Bari mu yi dubi kan batun.

Jaridar Haareth da ake bugawa a isara’ila tace jami’an isara’ila sun yi watsi da batun yin aiki da majalisar samar da zaman lafiya a yankin gaza, kuma ta sanarwa da Washington da lamarin, adaidai lokacin da jaridar times ta isra’ila kuma ta buga labari a jiya jumaa cewa kungiyar Hamas  ta sanarwa masu shiga tsakanin cewa ba za ta mika makamanta ba karkashin ci gaba da daukar mataken soji da isra’ila ke yi a yankin gaza

jaridar ta isra’ila ta nakalto daga wani daga cikin jami’an diplimasiya na kasashen dake shiga tsakani kan dakatar da bude wuta a gaza, bacin ran jakadan musamman na kasar Amurka Jared Kushner ya nunawa  fira ministan isra’ila Benjamin Natanyaho sai dai bai zama barazanar hana bayar da taimako idan har hare haren isra’ila basu tsaya ba

sai dai jami’in diplomaiyar da jaridar ba ta ambaci sunansa ba yace Amurka ta amince da tunani a jira sai bayan zaben da zaa yi a isra’ila a watan oktoba mai zuwa, kafin ta tantance matsayarta kan majalisar samar da zaman lafiya,

haka zalika jaridar haarez da ake bugawa a isra’ila ta bayyana cewa dangantaka tsakanin Natanyaho da Donald Trump  ta yi muni sosai , sakamakon sabanin da suke da shi  na cikin gida game da da yadda za’a gudar da ikon yankin Gaza

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted