Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta zargi Faransa da cewa tana da hannu a boren wasu sojojin kasar da su ka yi kokarin kifar da gwamanti ta hanyar kai wa fadar shugaban kasa hari.
Tashar talabijin ta gwamnatin kasar Nijar ta watsa bayanin da ya fito daga hukumar kasar a jiya Juma’a da a cikin ta zargi Paris da yunkurin juyin Mulki a makon da ya shude.
Wasu sojojin kasar ta Nijar sun kai hari a flin saukar jiragen saman a Yamai a ranar 29 ga watan Ogusta a wani yunkuri na kifar da gwamantin shugana Abdurrahman Thiani.
An rika jin kararrakin harbe-harbe a cikin birnin na Yamai da ya hada filin saukar jiragen sama na soja da kuma kusa da fadar shugaban kasa.
Kwana daya bayan haka ne mahukuntar kasar su ka sanar da cewa sun murkushe masu boren tare kuma da sake rike linzamin tafiyar da kasar.
Majalisar ministocin kasar ta jamhuriyar ta bayyana cewa; Da akwai bangarori da dama da suke a cikin wannan makarmashiya wacce Faransa ta jagoranci kitsa ta.”
Bayanin da aka fitar ya kuma ce; Da akwai kwararan dalilai da aka tattara da suke nuni da wadanda suke da hannu a wannan hari, kuma kasar ta Nijar tana da hakkin shigar da kara a gaban kotunan kasa da kasa.
Faransa wacce ba ta ji dadin korarta da wasu kasashen Afirka su ka yi ba, tana kokarin sake dawo da tsohon tasirinta a nahiyar ta kowace hanya.