Ma’aikatar lafiya ta kasar labanon ta bayyana cewa akalla mutane 3 sun mutu wasu guda 23 kuma sun ji mummunan rauni sakamakon sabon hari da sojojin isra’ila suka kai a kudanci da gabashin kasar labanon, kuma an sanar da wadanda suka jikkata ne bayan hare-haren da isra’ila ta kai a yankunan nabatia da kuma bekaa
gidan talabijin din almayadeen na kasar labanon ya rawaito cewa tankokin yakin isra’ila da jiragen yakin ta sun kai hare hare a nabati’a al-Fawqa, yayin da jirgin sama marasa matuki na isra’ila suka kai hari a kusa da garin kufr rommen inda ya kashe mutum biyu ,
sojojin isra’ila sun karbe iko da yankunan da suka rusa a al-mansuri da kuma yankunan dake wajen Zawtar al-sharqiya, a gabashin bekka ma isra’ila ta kai hari a garin ain al tinen, ma’akatar lafiya ta ce wadanda suka jikkata baa san adadinsu ba, komai na iya canzawa saboda yadda ake ci gaba da gano mutane da abin ya shafa
a watan yuni gwamnatin labanon da ta isra’ila sun cimma abin da suka kira yarjejeniya karkashin shiga tsakanin Amurka mai cike da rudani ,inda isra’ila za ta janye daga kudancin labanon tare da maye gurbinsu da sojojin labanon da kuma kwabe dammarar kuungiyar hizbullah
sai dai tuni kungiyar hizbullah tayi watsi da batun kwabe dammararta musamman bayan da isra’ila taki ficewa daga kudancin labanon