Ma’aikata A Najeriya Sun Bukaci A Kara Mafi Karancin Albashi

yanayin tsadar rayuwa ta sa ma'aikata a najeriya a kara albashi zuwa naira300,000

Ma’aikatan gwamnatin tarayya a ƙarƙashin inuwar kungiyar Federal Workers Forum (FWF) sun sake neman agajin gaggawa daga shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, da majalisar tarayya, inda suka bukaci a kara mafi ƙarancin albashi daga naira 70,000 zuwa naira 300,000

Wannan kiran ya zo ne a cikin wata wasika ta musamman da shugabannin kungiyar, Andrew Emelieze da Ogundele Ayodele, suka sanya wa hannu tare da aikawa ga shugabannin majalisar dokoki da sauran manyan jami’an gwamnati.

A cikin bukatun nasu, ma’aikatan sun bayyana cewa tsarin albashin da ake amfani da shi a halin yanzu ya daina tafiya daidai da yanayin tattalin arziki da tsadar rayuwa da al’umma ke fuskanta a faɗin ƙasar.

Baya ga neman karin mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata, kungiyar ta FWF ta kuma gabatar da shawarar sake fasalin albashin manyan ma’aikatan gwamnati, inda ta nemi a sanya mafi girman albashi ga ma’aikata da ke matakin daraja ta 17 zuwa  naira miliyan daya da rabi a kowane wata, domin samun daidaito da adalci a tsarin biyan kuɗi na ma’aikatan gwamnatin tarayya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted