Alkalin Alkalan Iran Ya Gabatar Da Jawabi A Wurin Taron “Brics” A Kasar India

Kiran A Daina Zaben Wadanda Za A Yi Wa Adalci Da Wadanda Ba Za A yi Wa ba
Alkalin Alkalan Iran

Alkalin alkalan kasar Iran Hujjatul-Islam Wal Muslimin Muhsini Iji wanda yake halartar taron shugabannin ma’aikatar shari’a na kungiyar “Brics” a birnin New Delhi na kasar Indiya, ya bayyana cewa; Bai kamata ce ana zabar wadanda za a yi wa adalci da wadanda ba za a yi wa ba, ko kuma shigar da siyasa a cikin harkokin sharia.”

Babban mai shari’a na kasar Iran Muhsini Iji ya kuma ce; a Wannan lokaci muna da bukatuwa da ganin an shimfida adalci,wanda kuma ba zai nama bisa zabin wadanda za a yi wa adalcin da wadanda ba za a yi ba.:

Haka kuma ya ce, ko kadan bai kamata ace ana yi wa al’ummu da kasashe adalci bisa la’akari da karfin da suke da shi ba.

Da yake Magana akan dokokin kasa da kasa alkalin alkalan na kasar Iran ya ce:

“Aikin yin doka da kuma aiki da ita, suna daga cikin muhimman ginshikan da suke samar da tsari, adalci da kuma ci gaba a cikin kowace al’umma.” Bugu da kari alkalin alkalan na Iran ya kuma ce:

” yadda gwamnatoci da kuma cibiyoyin kasa da kasa za su yi aiki da dokoki zai iya shawo kan da hana amfani da karfi da wuce gona da iri na wasu kasashe a duniya.”

Da yake Magana akan rawar da kungiyar ta “Brics” za ta taka a fagen tsarin siyasar kasa da kasa  da yake kafuwa, alkalin alkalan na jamhuriyar musulunci ta Iran ya ce: Kungiyar ta Brics tana a matsayin daya daga cikin kungiyoyin kawance na tattalin arziki da siyasa kuma tana da gagarumar  rawar  takawa a samar da sabon tsari a duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted