Dakarun Sojin Iran Sun Shawarci Amurka Da ta Fice Daga Yankin

iran ta bukaci su fice daga yankin yammacin asiya baki daya kuma su biya farashin harin da suka yi

Kakakin sojin kasar iran birgediya Ganar Mohammad Akraminiya ya ce kasar Amurka ta amince da abinda zai biyo bayan shawarar da ta yanke na kai hari kan kasa mai yanci kuma wayayya , kuma ta fice daga yankin yammacin asiya baki daya

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa na X a jiya juma’a Akraminiya ya ce kalubalen dake fuskantar sojojin Amurka a yankin da kuma matsalolin da alummar Amurka suke fuskanta ya samu asali ne daga matakin da Washington ta dauka na kaddamar da hari kan yantattar kasa, don haka mafita gareta shi ne ta amince da gaskiya ta biya farashi kuma ta fice daga yankin

kwamandan ya kara da cewa ficewar Amurka daga yanki zai taimaka sosai wajen samar da tsaro da zaman lafiya kuma zai kusanto da Amurkawa zuwa ga samun wadata

kasar Amurka da Isra’ila sun kaddamar da haramtacen hari kan  kasar iran a ranar 28 ga watan fabareru, kana kuma kwanaki 40 bayan nan wato a ranar 8 ga watan Aprilu an tilastawa makiya amincewa da dakatar da bude wuta a daidai lokacin da iran take ci gaba da tsayin daka kuma take mayar da martani mai karfi cikin nasara

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted