Shugaban kungiyar Tarayyar Afrika Ya Fara  ziyara a kasar Mali da nufin daidaita alaka

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Mahmoud Ali Youssouf, ya fara  ziyarar aiki ta kwanaki biyu a birnin Bamako fadar gwamnatin Mali, wadda ya fara a ranar

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka Mahmoud Ali Youssouf, ya fara  ziyarar aiki ta kwanaki biyu a birnin Bamako fadar gwamnatin Mali, wadda ya fara a ranar 12 ga watan Yuli, a matsayin ziyara irinta ta farko da wani babban jami’in kungiyar ya kai kasar ta yankin Sahel.

Tun a watan Yunin shekarar 2021, kungiyar Tarayyar Afirka ta dakatar da Mali daga dukkan harkokinta, bayan juyin mulkin soji da ya faru a kasar.

A yayin zaman a Bamako, shugaban na AU ya gana da Shugaban mulkin rikon kwarya na kasar, Janar Assimi Goïta, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi makomar kasar ta yankin sahel.

Babban abin da ya mamaye tattaunawar shi ne yadda za a bullowa matsalar tsaro da ta addabi yankin Sahel da kuma hanyoyin da kasar Mali za ta bi wajen komawa ga turbar dimokradiyya.

Baya ga tarukan gwamnati, babban jami’in na AU ya kuma ziyarci ofisoshin rundunar wanzar da zaman lafiya da sasanta rikici ta kungiyar Tarayyar Afirka a Mali da shiyyar Sahel MISAHEL da ke Bamako.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted