Mataimakin shugaban kasar Tanzania Emmanuel Nchombi ya kaddamar da saukarsa daga kan mukaminsa yana mai cewa; ya yi hakan ne saboda ya cikawa shugabar kasar fatanta.
Saukar mataimakin shugaban kasar na Tanzania ya zo ne makwo daya bayan da kafafen watsa labarun kasar su ka bayyana cewa da akwai sabani a tskaanin masu tafiyar da gwamnatin kasar.
A yayin zaben da aka yi na karshe Samira Suluhu Hassan ta lashe da kaso 98% na jumillar kuri’un da aka kada, kamar yadda hukumar zaben kasar ta bayyana.
Mataimakin shugaban kasar ya rubuta a shafinsa na sada zumunta cewa; “Na yanke shawarar sauka daga kan mukamina, da barin siyasa da kuma aikin gwamnati.”
Sakon da ya rubuta da harshen sawahili a shafin “Instigram” ya kunshi cewa; Zai fara aiki ne daga ranar 4 ga watan Satumba.”
Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugabar kasar ta Tanzania akan wannan batu.
‘Yan hamayyar siyasar kasar da su ka kauracewa zabe, suna zargin shugaba Suluhu Hassan da mayar da kasar kan turbar kama-karya irin ta wanda ta gada akan gadon mulkin kasar.
A karshen makon da ya shude ne aka gabatar da jagoran ‘yan hamayya Lissu a gaban shari”a domin ya amsa wasu tambayoyi masu alaka da shariar da za ayi masa a nan gaba bisa bisa zargin cin amanar kasa saboda ya yi kara a kaurewa zabukan da aka gudanar.