Cibiyar “SMB Intelligence” wacce ta gudanar da bincike akan kudaden da masu garkuwa da mutane suke samu daga iyalan wadanda su ka yi garkuwa da su, ta ce barayin dajin sun tara dukiya mai yawan gaske.
Rahoton wanda aka fitar da shi ayau Laraba, ya kunshi cewa; Masu dauke da makamai sun sami kudaden da sun kai Naira biliyan 7.78 wanda ya kai kwatankwacin Dala miliyan 5.8 a cikin shekara daya.
Rahoton ya kuma ce; Daga watan Janairu 2025 zuwa Yuni 2026 kadai, an sace mutane 7825 da hakan yake nufin cewa an sami karuwar sace mutanen da kasu 66% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Haka nan kuma rahoton ya ce a tsakanin wannan adadin na mutanen da aka sace, an kashe 1142,daga cikin da akwai fararen hula 895.
Dangane da yawan kudaden da aka bayar a wannan shekarar idan aka kwatantasu da shekarun baya,an sami karuwarsu da kasu 3 % da yawan Naira biliyan 2.56,wanda ya yi kwatankwacin Dala miliyan 1.9.
Cibiyar dai ta dogara ne da rahotannin kafafen watsa labaru da tattaunawa da daidadikun mutane da lamarin ya faru da su da kuma bayanai da sauran mutane su ka sani.
Wani sashe na bayanin ya bayyana cewa kaso 99% na wadannan kudaden da aka bayar, kungiyar Bokoharam ce ta same su a yankin Arewa masu gabashin Nigeria. Sai dai kuma an fi sace mutane ne a yankin Arewa maso yammacin kasar. Wannan rahoton ya fito ne dai adaidai lokacin da shugaban kasar Nigeria Bola Ahmad Tinubu ya sanar da ceto da mutane 600 da aka yi garkuwa da ku a Jahar Niger.