Shugaban kasar Tunusiya Qais Sa’id ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu da kuri’u kashi 90.69% da aka kada
Hukumar zaben Tunisiya ta sanar a jiya Litinin cewa: Qais Sa’id, wanda ke rike da madafun iko a kasar tun daga shekara ta 2021, ya sake lashe zaben shugaban kasa a karo na biyu bayan da ya samu kashi 90.69% na kuri’un da aka kada a kasar.
Sa’id ya samu kuri’u miliyan 2.4, yayin da abokin hamayyarsa da ke gidan kurkuku Al-Ayashi Zamal, ya samu kuri’u 197,000 wato (7.35%), shi kuma tsohon dan majalisar Dokokin Kasar Zuhair Al-Maghzawi ya samu kuri’u 52,000 (1.97%), wanda shi ne mafi karancin kuri’u tun bayan juyin juya halin da ya hambarar da gwamnatin Zainul-Abidine Ben Ali a shekara ta 2011.