Shugaban kasar Najeriya  Bola Tinubu Ya Ƙi Ganawa Da Jakadan Afirka Ta Kudu

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ki karbar wata tawaga ta musamman da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya aika najeriya kan hare-haren kyamar

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ki karbar wata tawaga ta musamman da Shugaban Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya aika najeriya kan hare-haren kyamar baki da aka sake kai wa ƴan Nijeriya da sauran ƴan Afirka a kasar Afirka ta Kudu.

Majiyoyin labarai sun ce tawagar, wadda Ministan Harkokin Ƙasa da Haɗin Kan Ƙasa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, ke jagoranta, ta isa Abuja a karshen mako dauke da sako daga Shugaba Ramaphosa.

Sai dai an umarci tawagar da ta je Ma’aikatar Harkokin Waje domin mika sakon ga ministan. Da aka tuntubi, mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya tabbatar wa yan jaridu faruwar lamarin.

Ya ce jami’an Ma’aikatar Harkokin Waje sun dauki wannan bukata a matsayin wadda ba ta dace ba.“Da farko dai, wakilin ya iso ranar Juma’a ba tare da sanar da gwamnatin Nijeriya tun da wuri ba. Ya dage cewa sai ya gana da Shugaban Ƙasa ranar Juma’a domin mika masa sakonsa.

Ya ƙara da cewa Shugaban Ƙasa ya umarci Ministan Harkokin Waje, Ambasada Enikanolaiye, da ya tattauna da wakilin tare da yi masa bayani daga bisani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted