Jami’ar Likitanci dake gundumar “Hurmuzgan” ta sanar da shahadar mutane biyu a sanadiyyar harin da Amurka ta kai wa tsibirin a daren jiya Laraba.
Sanarwar ta kunshi cewa; Amurka din ta kai harin ne akan rukunin gidaje mutane a cikin garin na “Qashm” kuma masu aikin agaji suna aikin fito da wadanda suke a karkashin baraguzai.
Ya zuwa lokacin da aka fitar da sanarwar an fito da shahidai biyu, kamar kuma yadda aka tseratar da kananan yara biyu masu shekaru 11 da 7,kuma tuni an kai su zuwa asibiti.
Sanarwar ta kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan shahidan,tare da cewa za ta yi aiki da dukkanin kayan da take da su domin taimakawa wadanda su ka jikkata.
A daren jiya Laraba ne dai Amurka ta kawo wa Iran jerin hare-hare a yankunan kudancin kasar da su ka haddasa asara ta rayuka da kuma dukiya.
Kamfanin dillancin labarun “Pars” ya ce, jiragen yakin Jamus da Faransa sun taimakawa Amurka wajen kakkabo makamai masu linzamin da Iran din ta harba akan sansanonin sojojin ‘yan ta’adda na Amurka a kasar Jordan.
Iran dai ta sha alwashin mayar da martani mai tsanani akan Amurka a yau Alhamis, da kuma duk kasar da ta taimaka mata wajen kawo harin.