Rahotanni sun bayyana cewa shugaban kasar china Xi Jinping ya ziyarci kasar koriya ta kudu a daidai lokacin da rikici yake kara Kamari a yankin domin kara karfafa dangantaka dake tsakanin kasashen biyu masu makwabtaka da juna,
shugaban kasar China ya isa birnin Pyonyang babban birnin koriya ta Arewa ne a yau litinin inda ya gana da takwaransa na koriya ta Arewa Kim Jung Un, kuma an daga tutocin kasashen guda biyu a manyan titunan birnin,
Ana sa ran shugabannin kasashen biyu za su tattauna kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da kuma huldodin kasa da kasa da kuma yadda za su yi hadin guiwa tsakanin kasashen biyu da kasar Rasha,
Ministan harkokin wajen kasar china yace taron zai yi musayar ra’ayi tsakanin shuwagabannin biyu kan dagantakar dake tsakaninsu. ya kara da cewa hakan zai kara tada hankali a yankin yammacin Asiya saboda yakin baya bayan da Amurka da isra’ila suka kaddamar kan iran da sauran kawayenta.
masu fashin baki kan harkokin siyasa sun yi hasashen cewa taron zai samar da wani tsari ga dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da ma sauran kawayensu, adaidai lokacin da dukkansu ke kokarin dawo da abokantakansu ta gargajiya a gaban yin takaddama da kasar Amurka.