Kasar Senegal, ta nuna goyan bayan ta ga gwamnatin Mali a yakin da ta ke yi da ta’addanci.
A yayin ziyarar da ya kai Bamako, Bassirou Diomaye Faye ya sake jaddada goyon bayan Senegal ga Mali a yakin da take yi da ta’addanci.
Ya kuma jaddada kudirin Dakar na karfafa hadin gwiwarta da Bamako dangane da kalubalen tsaro da ke addabar yankin Sahel baki daya.
Shugabannin kasashen biyu sun amince su karfafa hadin gwiwar tsaro, tattalin arziki, da na yanki.
Shugaban kasar Senegal kan kuma kuma shugaban kungiyar ECOWAS a wannan karo ya kuma yaba da kokarin da hukumomin Mali suka yi na dawo da zaman lafiya da tsaro, yayin da ya jaddada cewa barazanar ta’addanci a yanzu ta ketare iyakokin Mali.
“Senegal a shirye take ta tallafa wa Mali ta wannan mawuyacin hali,” in ji shi, yana mai kara da cewa zaman lafiyar yankin Sahel muhimmin abu ne ga dukkan kasashen yankin.
Shugabannin kasashen biyu sun nuna ra’ayoyi iri-iri kan batutuwa da dama kuma sun yi alkawarin farfado da hanyoyin hadin gwiwa na yankin, musamman a cikin Kungiyar Ci Gaban Kogin Senegal da Kungiyar Tattalin Arziki da Kudi ta Yammacin Afirka.
Ta hanyar nuna goyon bayanta ga Bamako tare da jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa a yankin, Dakar na neman ci gaba da tattaunawa da makwabciyarta yayin da take sake jaddada cewa yaki da ta’addanci ya kasance gama gari na kasashen Sahel.