Shekara ta biyu ke nan, Amurka tana hana shugaban hukumar Falasdinawa bizar shiga kasarta domin halartar tarukan Majalisar Dinkin Duniya
A shekara ta biyu a jere, Amurka ta ƙi ba wa Shugaban Hukumar Falasdinawa Mahmoud Abbas da tawagarsa takardar izinin shiga kasarta, wanda hakan ya hana su halartar taron Majalisar Dinkin Duniya da aka shirya gudanarwa a birnin New York a mako mai zuwa.
Wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar ta ce, “Amurka za ta tsawaita takunkumin da ya hana bayar da takardar izinin shiga ga membobin Kungiyar ‘Yantar da Falasdinawa da jami’an Hukumar Falasdinawa saboda gazawarsu wajen aiwatar da gyare-gyare, sabanin alkawuran da suka yi wa Amurka, da kuma ci gaba da ayyukansu da ke kawo cikas ga makomar zaman lafiya.”
Majiyoyin manema labarai da dama sun tabbatar da cewa: Shawarar da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yanke ta haɗa da Shugaba Mahmoud Abbas.
Ma’aikatar ta bayyana cewa ta sanar da Majalisar Dokoki cewa Kungiyar ‘Yantar da Falasdinawa da Hukumar Falasdinawa “sun sake gaza cika wajibcinsu a ƙarƙashin Dokar Alƙawarin PLO ta 1989 da Dokar Alƙawarin Zaman Lafiya ta Gabas ta Tsakiya ta 2002.”