Kwamandan Rundunar IRGC: Iran Zata Kalubakanci Makiyanta

Kwamandan Rundunar Sojojin Kasa ta Dakarun Tsaron Juyin Juya Hali ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren lissafi da makiya suka yi, za su fuskanci mayar

Kwamandan Rundunar Sojojin Kasa ta Dakarun Tsaron Juyin Juya Hali ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren lissafi da makiya suka yi, za su fuskanci mayar da martani mai ƙarfi

Kwamandan Rundunar Sojojin Kasa ta Dakarun Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran “IRGC” Birgediya Janar Karami ya bayyana cewa: Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da yardar Allah da goyon bayan al’ummar Iran masu daraja, gami da basira, da kuma wadanda ke nan filin daga ko da yaushe, za su mayar da martani da karfi ga duk wani kuskure da makiya suka yi kan kasar Iran.

Kamfanin Dillancin Labaran Mehr na kasar Iran ya ruwaito cewa: Birgediya Janar Karami, kwamandan Rundunar Sojojin Kasa ta Dakarun Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci na Iran “IRGC”, ya ce a lokacin da ya kai ziyarar aiki zuwa tsibiran Tekun Farisa cewa: Sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, da yardar Allah da goyon bayan al’umma masu Daraja da basira, da kuma wadanda ke nan a ko da yaushe a filin daga, za su mayar da martani da karfi ga duk wani kuskure da makiya suka yi kan kasar Iran. Ya kara da cewa: Tutar Annabin Musulunci a yau tana hannun manyan alo’ummar Iran masu daraja.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted