Sabon Jakadan Najeriya A Iran Ya Mika Takardar Kama Aiki

sabon jakadan iran a najeriya ya mika takardar kama aiki a iran ga shugaban kasar iran pezeshkiyan

Shugaban kasar iran ya yi kira da a kara kaimi wajen samun dangantaka mai karfi da kuma yin aiki tare da tarayyar najeriya ta fuskancin tattalin arziki, siyasa da kuma aladu tsakanin Tehran da birnin Abuja, yace kasashen biyu suna da muhimman abubuwa da za su iya kare dangantar dake tsakaninsu

Shugaban kasar yayi wannan kiran ne a lokacin ganawarsa da sabon jakadan najeriya a kasar iran Alh Hamza mohammad Salau lokacin da ya mika takardar kama aiki a birnin Tehran a matsayin sabon jakada, haka zalika yayi ishara game da kyakkayawar mahangar alummar najeriya game da kasar iran, kuma yayi kira ga sabon jakadan ya yi kokari wajen yin amfani da lokacinsa na jakada wajen karfafa dangantaka tsakanin iran da najeriya ta fuskancin tattalin arziki siyasa da kuma aladu

Da ya koma a bangaren ci gaba da aka samu a yankin shugaban iran yace rikicin da ke faruwa a yankin ya samu asali ne daga siyasar babakere na Amurka da HKI, don haka yayi kira ga kasashen musulmi da kada su bari gwamnatin isra’ila ta tunkuda yankin cikin rashin tsaro da rikici, kuma yace akwai bukatar kasashen musulmi su hada kansu wajen samar da tsaro da zaman lafiya

Ana shi bangaren sabon jakadan najeriya a iran ALH Hamza mohammad ya isar da gaisuwar shugaban najeriya bola Ahamd tinubu ga shugaban kasar iran da ma alummar iran, kuma ya mika ta’aziyar gwamnati game da shahadar jagoran juyin musulunci na iran shahid Ayatollah sayyid Ali khamina’I, kuma yayi alkwarin yin aiki tukuru wajen karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted