Yayin da hare-haren Isra’ila ke ci gaba da faruwa a yankin Gaza da kuma yadda ayyukan Isra’ila ke barazanar kawo cikas ga samar da kasar Falasdinu, Babban Sakatern Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a samar dauki mataki mai ma’ana.
Abin da ake kira tsagaita wuta a Gaza wanda bai hana kashe fararen hula ko kuma korar al’umma ba shi da wata fa’ida inji shi.
Wannan shi ne furicin da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya yi a wani taro na musamman da aka gudanar a hedkwatar Huukmar da ke New York gabanin Ranar Hadin Kai ta Duniya ga Al’ummar Falasdinu, wadda za a yi a ranar 29 ga Nuwamba.
A cikin wani jawabi da Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Amina Mohammed ta karanta a madadinsa, ya yi kira ga al’ummomin duniya da su cika alkawuran da suka dauka zuwa zahiri.
Yanayin ya fi muni a Gaza, inda aka kashe dubban mutane aka wargaza gidaje, makarantu, da asibitoci, tun daga watan Oktoban 2025.
Ya yi Allah wadai da fadada matsugunan Isra’ila ba bisa ka’ida ba, wanda hakan zai iya raba Yammacin Kogin Jordan gida biyu da kuma jefa rayuwar Falasdinu a cikin hatsari.
Ya yi gargadin cewa matkin amincewa da kasar Falasdinu ta fuskar diflomasiyya da aka yi a shekarar 2025 da kuma amincewa da sanarwar New York da Majalisar Dinkin Duniya ta yi ba su isa ba, ya kamata a kara, a yi amfani da shi don hana duk wani mamaye yankin, dakatar da ayyukan matsugunan, da kuma karfafa cibiyoyin Falasdinu.