Gwamnatin jihar Katsina ta arewacin Najeriya ta sanar da kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike kan wani fai-fan bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk Umar CON yana kokarin haikewa wata baturiya yar yawon bude ido.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Bala Salisu Zango PhD kwamishinan yada labarai na jihar ya ce gwamnatin Katisna ta dauki wannan zargi da mutukar muhimmanci kuma za ta yi duk mai yiwuwa don bankado gaskiyar lamarin.
Sanarwar ta ce an dorawa wannan kwamiti alhakin gudanar da bincike da kuma baiwa gwamnati shawara kan matakin da ya kamata ta dauka.
har ila yau Sanarwar ta kuma bukaci jama’ar Najeriya da su kaucewa yada jita-jita tare da jiran sakamakon binciken kwamitin da kuma matakin da gwamnati zata dauka.