Qalibaf: Babu Tattaunawa Da Amurka Har Sai Ta Amince Da Sharudda 7

shugaban majalisar shawara ta kasar iran yace babu wata tattaunawa tsakaninta da amurka sai ta amince da sharudda 7

Shugaban majalisar shawarar musulunci na kasar iran kuma jagoran tawagar tattaunawa mohammad baqeer Qalibaf ya bayyana cewa babu wani shirin fara wata tattaunawa da kasar Amurka har sai ta amince da sharudda 7 da iran ta shimfida

shugaban  ya fadi hakan ne a lokacin bude taron majalisar a yau talata inda yayi watsi da kalaman baya bayan nan da shugaban Amurka Donald Trump da sakataren baitil malin kasar Scott Bessent suka yi kuma ya bayyana su a matsayin barazana ce kawai, amma matsayin iran a fili yake kuma ba za ta canza ba.

Qaliban yana ishara ne game da barazanar da trump yayi a ranar lahadi da ta gabata inda yace mai yi yuwa ya bada umarnin kai sabbin hare hare kan kasar iran bayan sabuwar shekara idan Tehran bata cimma wata matsaya da Washington ba.

Yace ana ci gaba da kokarin diflomasiya wajen ganin an warware banbance- banbancen dake tsakanin sakamakon bijerewa da amurka ta yi da yarjejeniyar islam abad da aka cimma na islam abad, sai dai iran ta jaddada cewa babu wata yarjejeniyar diflomasiya da za’a cimma, matukar Amurka bata cika sharuddanta guda 7 ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted