Ana Tir Da Shirin Amurka Na Tura Makamai Samaniya

Kasashen sun ki amincewa da duk wani yunkuri na tura makamai a sararin samaniya.

Kasashen Iran, China, Rasha, Belarus, da Cuba sun yi Allah wadai da shirin Amurka na tura makamai a sararin samaniya, suna gargadin cewa hakan zai zama barazana ga zaman lafiya da tsaro na duniya, kuma yana iya kara ta’azzara barazanar amfani da makamai a sararin samaniya.

A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa da aka fitar a Geneva, a lokacin zaman kwamitin aiki na hudu na MDD kan Hana Gasar Makamai a Sararin Samaniya (PAROS), kasashen biyar sun bayyana matukar damuwarsu bayan sanarwar da Washington ta fitar a hukumance game da shirinta na tura makamai a sararin samaniya.

Sun dauki wannan shiri a matsayin wata alama a fili ta kara ta’azzara amfani da makamai a sararin samaniya da kuma babbar barazana ga kokarin kasa da kasa na hana gasar makamai a wannan fanni.

A cewar kasashen biyar, wannan ci gaban ya tabbatar da damuwar da aka dade ana yi game da da nufin mayar da sararin samaniya zuwa fagen daga da kuma wurin ayyukan soja, wanda zai kara hadarin fafata makamai a wannan yanayi.

Kasashen Sun ki amincewa da duk wani yunkuri na tura makamai a sararin samaniya, inda suka jaddada cewa dole ne dukkan kasashe su guji daukar irin wadannan matakai wanda barazana ne ga tsaro, kwanciyar hankali, da dorewar ayyukan sararin samaniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted