Faransa : Kungiyoyi Sun Sake Kiran Zanga-zanga

Kungiyoyin sun yi imanin cewa karin guraben karatu 20,000 da gwamnati ta sanar a manyan makarantu bai isa ba.

A Faransa, bayan shafe watanni biyu na zanga-zanga, Æ™ungiyoyin dalibai da na malamai a manyan makarantu sun sake kiran da a fito wani gangami a ranar 26 ga Nuwamba a ci gaba da matsin lamba wa gwamnatin kasar don samar da sabbin wurare da kuma daukar karin malamai a jami’o’i.

“Bayan makonni na gangami da ba a taba ganin irinsa ba, gwamnati ta kasa mangance matsalolin da suka dabaibaiye sha’anin ilimi a kasar,” in ji kungiyoyin a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa.

Kungiyoyin da kungiyar babbar Kwadigo ta CGT, sun yi imanin cewa karin guraben karatu 20,000 da gwamnati ta sanar a manyan makarantu ba su isa ba.

“Manufofin tsuke bakin aljihu na shekaru goma sun raunana jami’o’i, dakunan gwaje-gwaje, cibiyoyi, da ayyukan tallafi”.

 Kungiyoyin sun yi Allah wadai da lamarin, suna kira da a “kara yawan guraben aiki” da “ci gaba da matsa lamba ga gwamnati musamman kirkirar guraben karatu 150,000 a manyan makarantu.

Suna kuma kira da a kara tallafin karatu da albashin ma’aikata, suna mai jaddada cewa ma’aikatan gwamnati sun rasa fiye da kashi 16% na karfin saye saye tun daga shekarar 2017.

Baya ga zanga-zangar da aka shirya yi a ranar 26 ga Nuwamba, kungiyoyin kwadago suna kira da a yi yajin aiki a fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted