Hafsoshin Tsaro Sun Amince A Tura Dakarun Yaki Da Ta’addanci

hafsoshin tsaro na kungiyar Ecowas sun amince da a tura dakarun yaki da ta;addanci kafin shekara ta 2027

Kasashen kungiyar ECOWAS sun tsayar da watan Disamban shekara mai zuwa ta 2027, a matsayin lokacin da za su kaddamar da rundunar hadin gwiwar da za ta kunshi dakaru dubu 1,650 da suke kokarin kafawa don yaki da ta’addanci. An cimma matsayar ce bayan taron da manyan hafsoshin tsaron kasashen na ECOWAS suka yi a tsakanin 17 zuwa 19 ga wannan wata na Nuwamba.

Rundunar za ta mayar da hankali ne wajen dakile hare-haren ta’addanci, tsattsauran ra’ayi, da sauran manyan laifuka a yankin.

A matakin farko, ana sa ran rundunar za ta kunshi dakaru 1,650 kafin a fadada ta zuwa dubu 5. Baya ga dakile ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, shugabannin sun tattauna kan samar da kudaden aiki, kayan yaki, da kuma hada kai da kasashen Sahel makwabta domin wanzar da zaman lafiya a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted