Hamas Tayi Tir Da Kisan Babban Jami’in Tsaro Da Isra’ila Tayi A Gaza

kungiyar hamas ta yi tirda kisan babban jami'in tsaro da isra'ila tayi a yankin gaza kuma tace kafin yaki ne.

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar gwagwarmaya ta Hamas ta yi tir da matakin da gwamnatin sahyuniya ta dauka na kashe babban jami’in tsaron cikin gidan yankin gaza, ta ce sun yi hakan ne domin kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron yankin gaza adaidai lokacin da take ci gaba da yi wa falasdinawa kisan gilla

A cikin bayani da ta fitar a yau talata hamas ta ce mummunan kisan gillan da aka yi wa birgedier janaral Naeem mohammad abu Nahl kuma babban daraktan hukumar kula da tsaron cikin gida na yankin gaza a wani hari da isra’ila ta kai a yammacin  gaza  ta bayyana shi a matsayin babban laifin yaki, kuma an yi shi ne da nufin kai hari kan alummar falasdinu da kuma raunana tsaron cikin gidan zarin gaza

Hakazalika kungiyar Hamas ta kara da cewa  harin wani yunkuri ne na lalata kokarin da ake yi na aiki da yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan oktoban shekara ta 2025 wanda aka yi don kawo karshen yakin kisan kare dangi da isra’ila ta fara a watan oktoban shakera ta 2023 da yayi sanadiyar mutuwar akalla faladsinawa 75000 a yankin gaza.

daga karshe kungiyar Hamas tace abu Nahl yana da dogon tarihin aiki, kuma ya taka rawar gani wajen kula da tsaro da kare yankin gaza, a lokacin yakin kisan kiyashi da isra’ila ta kaddamar a yankin

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted