Babban kwamandan dakarun kare juyin musulunci na iran major janaral Ahmad vahidi ya yi barazanar cewa duk wani yaki da za’a yi a nan gaba to ba ruwansa da iyakoki a yankin, don haka dakarun sojin kasar sun shirya tsafa don fuskantar duk wata barazana
Babban kwamanda yayi wannan bayani ne a gefen taron ranar dakarun sa kai na kasa wato basij karo na 8,a yau talata yana mai cewa ya kamata makiya sun fahimci cewa yaki da za’a yi a nan gaba ba dole bane ya kasance ya tsaya a iya yankin , kuma dakarun kare juyi na rike da ikon kula da yankin baki daya kuma suna shirye fiye da kowanne lokaci a baya
Vahidi ya soki ci gaba da kasancewar sojojin Amurka a yankin, ta ce babban burin Washington shi ne ta mamaye kasashe da kuma samun cikakken ikon kula da fadin yankin baki daya, domin ci gaba da kasancewar sojojin Amurka a yankin ya samo asali ne daga kwadayi kuma ba ta damu da muradu ko damuwar kasashen yankin ba
Kasar Amurka da isra’ila sun kaddamar da yakin na farko kan kasar iran da ya dauki kwanaki 12, a watan yulin shekara ta 2025, yayin da ta kaddamar da na biyu kuma ta fara a ranar 28 ga watan fabareru da ya kwashe kwanaki 40, kuma an dakatar da shi a watan aprilun shekara ta 2026