Sanarwar da dakarun kare juyin musulunci su ka fitar ta kunshi bayani akan cewa sun kai hare-haren mayar da martani ga Amurka akan sansanoninta na soja Ruwa a Bahrain da safiyar yau Laraba. Sanarwar ta ce harin mayar da martani ne akan hare-haren da Amurka ta kawo wa tsibiran Iran na Jask, sirik da Qashm da suke a gundumar Hurmuzgan a kudancin Iran.
Bugu da kari, sanarwar ta ce harin an kai shi a cikin hadin gwiwa na dakarun kare juyi da kuma sojoji, tare da gargadin cewa idan Amurkan ta sake yin wata tsokanar to za ta fukanci martani mai tsananin gaske.
A wani rahoton da kamfanin dillancin labarun “Mehr” ya nakalto daga dakarun kare juyin musulunci ( irgc) ya bayyana cewa; sun kai hare-hare da makamai masu linzami akan wurare 4 na ajiyar jiragen Amurka samfurin F-35 da cibiyar bayar da umarni ta sojan Amurka a garin Azraq na kasar Jordan. Sanarwar ta kuma ce harin ya yi sanadiyyar rusa wuraren ajiya jiragen yakin na Amurka.
Harin na safiyar yau dai yana a matsayin martani ne ga hare-haren da Amurka ta kawo wa tsibirun Iran, bisa zargin cewa Iran ta kakkabo jirginta mai saukar angulu samfurin Apachi.
A gefe daya, dakarun Iran sun harbo jiragen Amurka marasa matuki samfurin “Mq9” a yankin Hurmuzgan.