Rundunar tsaron juyin juya hali ta mayar da martani ga harin da Amurka ta kai ta hanyar kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke yankin
Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta sanar da safiyar yau cewa ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da suke Jordan, Bahrain, da Kuwait.
A cikin sanarwarta ta farko, Rundunar tsaron juyin juya halin Musulunci ta IRGC ta tabbatar da cewa: A matakin farko na martanin da ta mayar kan hare-haren Amurka, mayakanta sun kona wasu manyan rumbunan makamai masu linzami da wuraren adana mai a sansanin sojojin sama na Yarima Hassan da ke Jordan bayan sun kai musu hari da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki.
A cikin sanarwarta ta biyu, Rundunar tsaron juyin juya hali ta IRGC ta sanar da lalata muhimman cibiyoyin gyaran jiragen sama masu saukar ungulu, a wurin ajiye jiragen yaki na P-8 na lantarki, da kuma cibiyar bada umarni da kula da jiragen sama marasa matuka ciki na sojojin Amurka a sansanin sojojin sama na Sheikh Isa da ke Bahrain.
A cikin sanarwarta ta uku, Rundunar tsaron juyin juya hali ta IRGC ta tabbatar da lalata tankunan mai da tsarin tsaron iska na Patriot a sansanin sojojin Amurka da ke Ali Salem a kasar Kuwait, da kuma tsarin radar na FPS a sansanin sojojin sama na Ahmed Al Jaber. Sanarwar ta kammala da cewa ana ci gaba da gudanar da ayyukan gwarazan Iran jarumai a matsayin ramuwar gayya.