Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci Ta Sanar Da Rufe Mashigar Hormuz

Rundunar tsaron juyin juya hali ta sanar da rufe mashigar tekun Hormuz gaba daya har sai an dage matakin killace yankin da Amurka ta sanya

Rundunar tsaron juyin juya hali ta sanar da rufe mashigar tekun Hormuz gaba daya har sai an dage matakin killace yankin da Amurka ta sanya

Rundunar Tsaron Juyin Juya Halin Musulunci (IRGC) ta sanar da cewa: Za a rufe mashigar ruwan Hormuz daga ranar Asabar da rana har sai an dage takunkumin da sojojin ruwan Amurka suka sanya wa jiragen ruwa da tashoshin jiragen ruwa na Iran.

A cikin wata sanarwa da aka fitar da yammacin Asabar, rundunar IRGC ta ce, “a kwanakin nan jiragen ruwa sun ratsa mashigar ruwan Hormuz a karkashin kulawar rundunar da kuma hadin gwiwarta, bayan sanarwar Jamhuriyar Musulunci cewa za ta bar jiragen ruwan fararen hula su ratsa ta mashigar Larak.”

Sanarwar ta kara da cewa, “Makiya Amurka ta karya alkawarinta a karkashin yarjejeniyar tsagaita wuta, kuma bata dage takunkumin da aka sanya wa jiragen ruwa da tashoshin jiragen ruwa na Iran ba.”

Rundunar IRGC ta kara da cewa: Za a rufe mashigar Ruwan Hormuz daga ranar Asabar da rana har sai an dage takunkumin, tana gargadin dukkan nau’ikan jiragen ruwa da su guji yin duk wani motsi daga tasoshinsu a Tekun Farisa da Tekun Oman.

Rundunar ta IRGC ta jaddada cewa: Kusantar mashigar Hormuz za a yi la’akari da ita a matsayin hadin gwiwa da abokan gaba, kuma duk wani jirgin ruwa da ya karya wannan umarni za a kai masa hari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted