Mutane 16 sun mutu, wasu da dama kuma sun ɓace bayan wani ginin gidaje da ya ruguje a yammacin birnin Gaza
Falasdinawa 16, ciki har da yara da mata, sun mutu, wasu 25 kuma sun jikkata, yayin da wasu mutane kimanin 100 suka ɓace ko kuma suka makale a ƙarƙashin baraguzan ginin, bayan da wani gini na gidaje ya ruguje a yankin masana’antu a kudu maso yammacin birnin Gaza. Ginin yana matsaiyin matsugunin mutane da dama da suka rasa matsugunansu.
Gidan mai hawa shida, wanda harin bam na Isra’ila ya lalata a lokacin yaƙin, ya ruguje da sanyin safiyar Laraba a kan mazaunansa da ke barci, da kuma kan tantuna da ke kusa, a cewar wani wakilin gidan talabijin na Al Jazeera.
Rahotonni sun bayyana cewa: A baya, rundunar tsaron farar hula ta sami nasarar gano gawawwaki 9, ciki har da yara da mata, tare da ceto mutane 14 da suka ji raunuka, yayin da yawancinsu har yanzu ba a gan su ba ko kuma suna ƙarƙashin baraguzana gini.