Zaban Iran A Kwamitin Hukumar IAEA Ya Kunyata Amurka

Wakilin Iran na Dindindin a Ƙungiyoyin Ƙasa da Ƙasa a Vienna ya bayyana cewa: Amincewa da zaman Iran memba a babban kwamitin taron Hukumar IAEA

Wakilin Iran na Dindindin a Ƙungiyoyin Ƙasa da Ƙasa a Vienna ya bayyana cewa: Amincewa da zaman Iran memba a babban kwamitin taron Hukumar IAEA wani babban shan kaye ne ga bakar siyasar Amurka

Jakadan Iran kuma Wakilin Dindindin a Ƙungiyoyin Ƙasa da Ƙasa a Vienna, Reza Najafi, ya nuna adawar Amurka ga kasancewar Iran a cikin Babban Kwamitin Taron Hukumar  IAEA, yana mai cewa: “Bayan zaɓen sirri da goyon bayan ƙasashe da dama, Taron ya amince da zama memba na Jamhuriyar Musulunci ta Iran a cikin wannan kwamiti, wanda hakan ya zama wani koma-baya na bakar siyasar Amurka.”

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Mehr, Najafi ya shaida wa manema labarai cewa: “Taron ya haɗa da kwamiti mai suna ‘Babban Kwamiti,’ wanda aikinsa shine sake duba ajandar shirin tarurruka da takardun shaida.”

Ya ƙara da cewa: “Ƙungiyar Gabas ta Tsakiya da Kudancin Asiya (MESA), wata ƙungiya ta yanki, ta zaɓi Jamhuriyar Musulunci ta Iran don zama memba a wannan kwamiti a taron, kuma an shirya amincewa da zama memba na Iran. Amma Amurka, ta ci gaba da nuna adawarta a fili da kuma ra’ayin cusgunawa Iran ta fito ta nuna adawarta na kasancewar Iran a cikin Babban Kwamitin, don haka ta tilasta wa Taron ya jefa ƙuri’a a kan lamarin.”

Najavi ya ci gaba da cewa: “Ƙasashe da dama, don goyon bayan matsayin Iran, sun nemi a kada kuri’a a ɓoye.” An gudanar da zaɓen, kuma a ƙarshe taron ya amince da kasancewar Iran a cikin Babban Kwamitin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted