Rezaei: Babu wata tattaunawa har sai an cika sharuddan Iran

Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, ya tabbatar da cewa lamurra da suka  shafi kasuwannin mai da mashigar ruwa mai mahimmanci

Rezaei: Babu wata tattaunawa har sai an cika sharuddan Iran

Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran, Manjo Janar Mohsen Rezaei, ya tabbatar da cewa lamurra da suka  shafi kasuwannin mai da mashigar ruwa mai mahimmanci ta Hormuz sun canza gaba ɗaya a yankin.

A cikin wani rubutu da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, Rezaei ya bayyana cewa, “Ba za a yi wata tattaunawa ba kafin a cika sharuɗɗan Iran.”

Don haka ya bayyana matsayin tattaunawar Tehran a fili kuma ya jaddada cewa ba za a yi sassauci ba fiye da sharuɗɗan da aka ayyana.

Sakataren Majalisar Tsaron Ƙasa ta Iran ya yi kira da a guji fadawa cikin yaudara ta kalamai da ke fitowa daga Shugaban Amurka Donald Trump, yana mai cewa, “Kada ku yarda a yaudare ku da kalaman Trump masu karo da juna, daga ‘babu tattaunawa’ zuwa ‘muna shirye mu tattauna.'”

Manjo Janar Rezaei ya jaddada cewa ƙoƙarin gwamnatin Amurka na dakile tabarbarewar harkokin tattalin arziki da zirga-zirgar jiragen ruwa, da sauran matsalolin da suka shafi duniya sakamakon yakin da ya kaddamar, ba za su kawo karshe ba har sai ya yi biyayya ga sharuddan Iran.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted