Tehran ta yi Allah wadai da hana Mohammad Islami halartar taron IAEA

Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: kasashe mambobin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) dole ne su “tsaya kuma su yi

Hana Islami halartar taron IAEA

Kakakin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran Behrouz Kamalvandi, ya ce: kasashe mambobin Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) dole ne su “tsaya kuma su yi Allah wadai da cin zarafin Amurka.”

Kamalvandi ya bayyana hana shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran halartar taron IAEA a matsayin “wani aiki mai hatsari ga dukkan kasashe.”

Amurka ta hana shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran, Mohammad Islami, halartar taron IAEA a Vienna a wannan makon, bayan ta nuna adawa da bukatarsa ​​ta janye  takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta sake kakaba ma Iran a karkashin tsarin “snapback”, a cewar Reuters.

Eslami ya shirya halartar taron da kuma yin jawabi, taron da a ka saba gudanarwa shekara-shekara na kasashen mambobin IAEA.

Iran ta bayyana a lokacin bude taron cewa Austria ta soke takardar izinin shiga kasar ga Eslami, wanda ta riga ta amince da hakan tun daga farko.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghaei ya tabbatar da cewa mika fayil ɗin nukiliya na Iran ga Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ba shi da tushe, yana mai cewa “Iran ba ta aikata wani laifi na rashin bin ƙa’ida ba.”

Baghhaei ya ƙara da cewa “idan hukumar tana da lamiri na adalci komai karancinsa, to da ta yi  Allah wadai da hare-haren Amurka da Sahyuniywa a kan Iran da cibiyoyinta na nukiliya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted