Rahotani sun bayyana cewa kasar rashi ta yi gargadin cewa tana shirye shiryen kai munanana hare hare kan cibiyar samar da makamashi na kasar Ukrain, kuma ta bayyana shi a matsayin wani martani na kai tsaye na hare haren da kasar ukrain ta kai a cibiyoyin makamashinta.
Ministan tsaro na kasar rasha ya bayyana cewa dakarun sojin kasar rasha sun fara shirye shiryen kaddamar da hare hare mai cin dogon zango kan cibiyoyin makamashin kasar Ukrain, a cikin bayanan da ya wallafa a shafinsa na telegram ministan yace wannan matakin martani ne kan hare-haren da kasar Ukrain ta kai a wuraren fararen hula da kuma cibiyar mai da makamashi na rasha
Wannan gargadin yazo ne wata guda bayan kara rincabewar yaki tsakanin bangarorin biyu inda aka kai harin kan wuraren kasuwanci da na mai da naurorin mashigar ruwa da jiragen ruwa da ya jawo mutuwar fararen hula da dama,
Shugaban kasar Rasha Viladmir Putin ya yi irin wannan gargadin a makon jiya, yace hare haren da kasar Ukrain takai kan muhimman wurare a kasar Rasha ya bude hanyar da ta ba da damar mayar da martani wanda zai shafi cibiyoyin tattalin arziki mafi muhimmanci a kasar ta Ukrain