Shugaban kasar Iran ya gana da Fira Ministan Pakistan a kasar Kyrgyzstan a gefen taron Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai (SCO)
Shugaban kasar Iran Mas’oud Pezeshkian ya gana da Fira Ministan Pakistan Shahbaz Sharif a ranar Litinin a gefen taron Kungiyar Hadin Gwiwa ta Shanghai (SCO) da kuma taron Shanghai Plus a Kyrgyzstan.
Kamfanin dillancin labaran “IRNA” ya ruwaito cewa: Shugaba Pezeshkian da Fira Minista Sharif sun tattauna sabbin ci gaban da aka samu a dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma hadin gwiwa gami da hanyoyin inganta huldar hadin gwiwa.
Bangarorin biyu sun yi nazari kan sabbin ci gaban da aka samu da kuma hanyar hadin gwiwa tsakanin Tehran da Islamabad, inda suka jaddada bukatar amfani da damar da ake da ita don bunkasa da zurfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu a fannoni daban-daban.